Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ra'ayi Riga: Ko me ya sa cin hanci da rashawa ke karuwa a duniya?

Image caption Tambarin kungiyar Transparency International

Sakamakon wani bincike da Kungiyar tabbatar da adalci ta Transparency International ta gudanar, ya nuna cewa matsalar cin hanci da rashawa ta kara muni a kasashe daban-daban na duniya a cikin shekaru biyun da suka wuce.

Rahoton, wanda aka wallafa a cikin wannan makon, ya nuna cewa matsalar ta fi kamari ne a wasu muhimman bangarorin aikin gwamnati da ake bai wa amanar al'umma, ciki har da 'yan sanda da bangaren shari'a.

To ko hakan ya na nufin yakin da gwamnatoci ke ikirarin suna yi da matsalar ba ya wani tasiri kenan? Ta yaya magance matsalar a zahiri?