Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Gane Mini Hanya: 'Yan gudun hijiran Najeriya a Bosso

A jamhuriyar Nijar dubban 'yan gudun hijira ne daga arewacin Najeriya suka kwarara cikin jihar Diffa mai makwabtaka da Najeriyar.

Hakan ya faru tun bayan lokacin da sojojin Najeriya suka kaddamar da hare- hare kan sansanonin 'ya'yan kungiyar Jama'atu AhlisSunna lidda'awati wal jihad da aka fi sani da Boko Haram a jihohin Borno da Yobe.

Rahotanni dai sun ce yawan 'yan gudun hijiran, wadanda suka hada da mata da kananan yara, sun kai dubu shida.

'Yan gudun hijiran, wadanda galibinsu ke garin Bosso na samun kulawa daga hukumomin Nijar da kungiyoyin agaji da kuma mazauna garin na Bosso.