Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ra'ayi Riga: Tsarin zuwa aikin Hajjin bana

Image caption Mahajjata a Makka

Yanzu haka dai, wasu jihohin Najeriya sun yanke shawarar cewa maniyattan da ba su taba yin aikin Hajji ba ne zaa fifita wajen bada kujerun aikin Hajjin bana.

Wannan dai ya biyo bayan matakin da Hukumomnin Saudiyya suka dauka ne a cikin watan Yunin da ya gabata na takaita yawan wadanda za su yi aikin Hajjin bana daga kasashen waje da kashi 20 daga cikin 100.

Hukumomin na Saudiyya dai sun ce sun dauki matakin ne saboda ayyukan da suka ce suna yi na fadadawa da kuma gyare-gyare a harami.