Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ra'ayi Riga: Rikicin Syria

Image caption Har yanzu Shugaba Assad na da magoya baya

Yanzu haka dai kasashen duniya na cigaba da kai-kawon diplomasiyya, domin gano bakin zaren rikicin Syria.

Kasashen sun kara farga da illar rikicin ne, bayan da a kwanan nan daruruwan mutane suka hallaka, a harin da ake zargin na makamai masu guba ne, wanda aka kai a wasu unguwannin kewayen Damascus babban birnin kasar, wadanda ke hannun 'yan tawaye.

Tuni kasashe irinsu Birtaniya da Amirka suka dora alhakin hakan a kan gwamnatin Shugaba Assad, su ke kuma neman a dauki matakin soja a kan Syriar.

Sai dai wannan yunkuri na Burtaniya ya gamu da cikas, bayan da a jiya majalisar dokokin kasar ta kada kuriar kin amincewa da matakin.

A daya bangaren kuma, kawayen Syria, irinsu Rasha da China, wadanda ke zargin 'yan tawaye ne suka kai harin, suna kira ne a jira rahoton sufetocin majalisar dinkin duniya da suka je Syriar don binciken lamarin, kafin a dauki duk wani mataki.