Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Gane Mani Hanya: Hausawa a Ingila

Kusan babban abinda ke jan hankalin mutane idan suka samu kansu a wuri, ko tsakiyar al'ummar da ba ta su ba, shi ne bambancin kabila, al'adu da kuma addini a wasu lokutan. Al'ummar Hausawa da ke zaune a nan Burtaniya basu tsira daga wannan kalubale ba.

Don haka ne ma wannan batu, ya kasance a cikin manyan abubuwan da aka tattauna a kansu, a lokacin babban taron kungiyar Musulmi mazauna Burtaniya na bana, wanda aka yi a karshen makon jiya, a garin Coventry.

Kuma kamar yadda za ku ji a wannan tattaunawar da Naziru Mikailu ya shirya mana da wasu daga cikin wadanda suka halarci taron, Hausawan na kewar gida.