Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Gane Mani Hanya: Sallar lasar gishiri a Nijar

A Nijar, a ranar litinin da ta wuce ce aka kammala bikin sallar makiyaya ko kuma 'Cure Salee', a garin Ingall na jihar Agades, a arewacin kasar.

An yin bikin ne a kowace shekara, inda makiyaya ke haduwa domin gabatar da matsalolinsu ga mahukunta, sannan dabbobin nasu su rika lasar wani gishirin da ke da alfanu ga lafiyarsu.

Makiyaya daga ciki da wajen Niger din ce suka halarci bikin, wanda Praministan Briji Rafini ya jagoranta.

kasar ta Nijar ne suka halarci wannan bikin.

Tchima Ila Issoufou, ita ta wakilce mu a Cure Salee, ga kuma tsarabarta a filin Gane Mani Hanya: