Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Harbe- Harbe a cibiyar kasuwanci a Kenya

An yi ta jin karar harbe-harben bindigogi da kuma fashewar abubuwa a rukunin shagunan da 'yan bindiga suka yi garkuwa da mutane a Nairobi.

Ana tsammanin maharan tsakanin 10 zuwa 15, wadanda ake tunanin 'yan Kungiyar Al-Shabab ne, har yanzu na cikin ginin yayin da aka shiga rana ta uku da aukuwar lamarin.

Fiye da mutane 69 sun mutu sannan wasu fiye da 170 sun samu raunuka.