Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Gane Mani Hanya 19/10/13

A Najeriya wani batu da yanzu haka yake janyo kace-nace, shine shirin shugaba Goodluck Jonathan na shirya taron tattaunawa na kasa.

Shugaban ya ce, idan an yi taron, zai mika sakamakonsa ga majalisar dokokin tarayya domin aiwatarwa.

Wasu 'yan kudancin Najeriyar dai sun jima suna kiran sai lallai a yi wannan taron, wanda a ganinsu zai bada zarafin warware dimbin matsalolin da suka addabi kasar. Amma a cewar masu adawa da taron kasar, da lauje a cikin nadi.

Hon. Yusuf Maitama Tuggar, dan siyasa a Najeriya, kuma mai hada-hadar man petur, ya ziyarce mu a nan BBC, kuma Isa Sanusi ya nemi jin ra'ayinsa a kan taron kasar, da kuma wasu batutuwa.