Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ra'ayi Riga:Wadanne kalubale mata ke fuskanta?

To yau wata guda kenan da BBC ke watsa shirye-shirye na musamman a kan irin kalubalen da mata ke fuskanta a wannan karni na ashirin da daya.

Mun gabatar maku da rahotanni da hiraraki da mata masu fama da matsanancin talauci, da matan da suka yi fice ta fuskar ilimi da tattalin arziki, da matan da suka kasance kallabi tsakanin rawunna a fagen siyasa, da dai sauransu.

Hakan na faruwa a daidai lokacin da rahoton shekara-shekara na kungiyar kula da tattalin arziki ta duniya (World Economic Forum) ke cewa, a shekarar da ta wuce, ratar da ke akwai tsakanin maza da mata ta dan ragu - amma ba a ko'ina ba.

Wasu kasashen, musamman a yankin gabas ta tsakiya da arewacin Afirka ma, koma baya suka fuskanta.