Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Gane Mani Hanya: Kalubale kan aikin likita

A wata Oktoba ne wata cibiyar likitoci da suka kware wajen tsara manhajar aikin likita, da ma sauran fannoni da suka shafi aikin kula da lafiya, ta gudanar da wani taro a London. An shirya taron ne domin duba kalubalen da aikin likitar ke fuskanta saboda sauye-sauye na zamani, da nufin canza shi domin ya dace da zamanin. Farfesa Ibrahim Inuwa na jami'ar Sultan Qaboos dake Oman, na daga cikin mahalarta taron, kuma sun tattauna da Ahmad Abba Abdullahi game da taron, da kuma matsalar aikin likita a Nijeriya.