Wasu da suka kamu da cutar kwalara
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ra'ayi Riga: Akan cutar amai da gudawa a Najeriya

A Najeriya kusan kowacce shekara cutar amai da gudawa tana hallaka rayuka da dama, yawancinsu kuma masu karamin karfi. Bana ma ya zuwa yanzu cutar ta hallaka mutane kusan casa'in a jihohi daban-daban.

To ko wanne hali ake ciki dangane da irin barnar da wannan cuta take yi? Kuma ma me yasa ta ki ci ta ki cinyewa a Najeriyar?