Shugaba Goodluck Jonathan na Nijeriya
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ra'ayi Riga: kara wa'adin dokar ta-baci

Image caption Jami'an tsaro a Nijeriya

A jiya ne Majalisar dattawan Nijeriya ta amince da bukatar da shugaban kasar, Goodluck Jonathan, ya mika mata, na kara wa'adin dokar ta bacin da ya sanya a jihohin Borno, da Yobe da Adamawa.

A ranar laraba ne dai shugaban kasar ya mika wannan bukata a bisa dalilan da ya ce matsalar hare-haren 'yan kungiyar Boko Haram ke ci gaba da kaiwa a wasu sassan jihohin, da ke haddasa asarar rayukan jama'a da dama.

Sai dai yayin da wasu ke cewa daga lokacin da aka kafa dokar-ta-bacin an samu ci gaba a yunkurin karya lagon 'yan kungiyarta Boko Haram , akwai kuma masu ganin cewa al'amurra ma sun kara tabarbarewa ne.