Shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ra'ayi Riga: Kasafin Kudi da matsalar aiwatarwa a Najeriya

Image caption Shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya

A mako mai zuwa ne ake sa ran shugaban Najeriya Dr Goodluck Jonathan zai gabatar wa majalisun dokokin tarayyar kasar kasafin kudi na shekara ta 2014.

Kasafin kudi dai abu ne da gwamnatocin kasashe kan gabatar domin dora harsashen tafiyar da harkokin tattalin arzikinsu a tsawon shekarar da abun ya shafa.