Zabe a Nigeria
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ra'ayi Riga; Nazari kan zaben Anambra

Image caption Zabe a Nigeria

Har ya zuwa yau din nan dai al'umar Naijeriya , ba ma jihar Anambra ba, na ci gaba da zaman jiran sauraron sakamakon zaben Gwamnan Jihar da aka yi ranar Asabar da ta gabata a jihar , zaben da jam'iyyu 23 suka tsaya takara. Wannan zabe, wanda ake yi wa kallon, zakaran gwajin dafi na auna shirye shiryen zaben shekara ta 2015, ya wuce ya bar baya da kura, domin kuwa har yanzu ba a bayyana wanda yayi nasara a zaben ba, duk da cewar an bayyana yawan kuri'un da kowane dan takara ya samu.