Ana ci gaba da alhinin rashin Nelson Mandela
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ra'ayi Riga: Rayuwar Marigayi Nelson Mandela

Cikin daren jiya ne dai Allah ya yiwa Nelson Mandela gwarzon yaki da mulkin wariya, kuma bakar fata na farko da ya mulki Afurka ta kudu rasuwa. Yayin gwagwarmaya da mulkin wariya ya yi zaman gidan kaso n shekaru 27, kuma ya rasu ne yana dan shekaru 95. To yaya rayuwarsa ta kasance? Kuma wanne darasi za'a koya daga rayuwar Nelson Mandela?