Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Gane Mani Hanya 21/12/13

A Nijeriya, daya daga cikin hanyoyin da hukumomi suka tanada wajen mika koke kan wani abin da wani dan kasa ya ji an yi masa ba daidai ba, ita ce a hanyar hukumar kula da koke koken jama'a ta kasa, wato National Public Complaint Comission, wadda aka kafa a 1975.

Sai dai kuma a 'yan shekarun nan kusan ba a cika jin duriyar wannan hukuma ba.

A filinmu na Gane Mini Hanya na wannan makon, Ahmad Abba Abdullahi ya tattauna da Dokta Mahmud Baffa Yola, daya daga cikin kwamishinonin wannan hukuma, mai kula da jihar Kano, lokacin da suka kai mana ziyara a ofishinmu na London, inda ya fara da takaitaccen tarihin hukumar.