Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Gane Mani Hanya 05/04/14

A Nigeria wakilai sama da 400 ne ke ci gaba da halartar babban Taron kasar.

Galibin batutuwan da wakilan suka fi yin tsokaci akai dai sun hada da tabarbarewar sha'anin tsaro da yaki da cin hanci da rashawa da batun kabilanci da dai sauran su.

Yayinda wasu ke sukar taron, gwamnatin Nigeriar na ikirarin cewa taro ne da zai duba matsalolin kasar domin nema ma ta kyakyawar makoma .

Ibrahim Mijinyawa wanda ke halartar taron ya hada mana rahoto na musamman game da shi.