Marigayi Sarkin Kano, Ado Bayero, a wurin wani taro
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ra'ayi Riga: Rayuwar Sarkin kano da gudumawar sarakuna a ci gaba

An yi jana'izar Mai martaba Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero, wanda Allah Ya yi wa rasuwa.

A filin namu na ra'ayi Riga zamu duba rayuwar marigayi Sarkin Kanon , da kuma irin gudunmawar da Sarakunan gargajiya ke bayarwa ga ci gaban al'umma.

Marigayin wanda ya rasu yana da shekaru tamanin da uku ya shafe 'yan shekarun nan yana fama da jinyar da ta sha kai shi kasashen waje neman magani.