Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Gane Mani Hanya 05/07/14

Kawo yanzu duka 'yan arewacin Nigeria kusan dari biyar da aka tsare a jihar Abia a kan hanyar su ta zuwa kudancin kasar an sallame su sun koma gida.

Sojoji ne dai suka kama mutanen sannan aka tuhume su ko suna da alaka da kungiyar Boko Haram.

Su dai hukumomin Nigeria na cewa sun kama wani babba a kungiyar ta Boko Haram cikin mutanen, koda yake har yanzu ba su bayyana ko wanene aka kama ba.

Mafi yawan mutanen da aka kama dai 'yan jihar Jigawa ne, kuma Wakilin mu Yusuf Ibrahim Yakasai ya tattauna da su da hukumomin jihar bayan da aka sako rukunin farko, ga kuma rahoto na musamman da ya hada mana kan wannan batu.