Kwanaki 90 da sace 'yan matan Chibok

Kwanaki 90 kenan cif-cif da 'yan Boko Haram suka sace 'yan mata dalibai su 276 a Chibok da ke jihar Borno a arewacin Nigeria.

A ranar 14 ga watan Aprilu 2014 'yan Boko Haram suka shiga da mota suka sace 'yan mata fiye da 200 da bakin bindiga a makarantar sakandaren Chibok a arewa maso gabashin Nigeria
Bayanan hoto,

A ranar 14 ga watan Aprilu 2014 'yan Boko Haram suka shiga da mota suka sace 'yan mata fiye da 200 da bakin bindiga a makarantar sakandaren Chibok a arewa maso gabashin Nigeria

Bayanan hoto,

Sace 'yan mata 276 'yan makaranta a Nigeria ya janyo zanga zanga a sassan duniya, inda 'yan kungiyar Bring Back Our Girls masu fafutukar ganin an kubutar da 'yan matan suke matsin lamba ga gwamnati ta ceto yaran da rayukansu.

Bayanan hoto,

Mai fafutukar kare 'yancin Ilmin mata Malala Yousafzai wadda ta tsira daga harbin da 'yan Taliban suka yi mata saboda ta na da'awar cigaban Ilmi ta bi sahun maudu'in #Bringbackourgirls.

Bayanan hoto,

Kasashen duniya sun yi kakkausar suka ga sace 'yan matan. Uwargidan shugaban Amurka Michelle Obama ta yi tir da sace 'yara 'yan mata da kungiyar Boko Haram ta yi.

Bayanan hoto,

Firaministan Birtaniya David Cameron da mai gabatar da shiri a tashar talabijin ta CNN Christiane Amanpour dauke da kwali da aka rubuta Bring Back Our Girls watau a dawo mana da 'yan matan mu, a wani shiri na Andrew Marr

Bayanan hoto,

'Yan makaranata a Afirka ta kudu da shugabannin addini sun shiga zanga zangar tsanaki domin nuna goyon baya ga 'yan mata 'yan makarantar Chibok wadanda aka sace fiye da wata guda a ranar Juma'a 16 ga watan Mayu 2014

Bayanan hoto,

Martha Mark mahaifiyar Monica Mark daya daga cikin 'yan makarantar Chibok a Nigeria da aka sace.

Bayanan hoto,

'Yan mata 28 daga cikin 'yan makarantar Chibok wadanda suka tsere wa Boko Haram sun je gidan gwamnati domin ganawa da gwamna Kashim Shattima a Maiduguri.

Bayanan hoto,

Wata daliba wadda ta tsere lokacin da 'yan Boko Haram suka afkawa makarantar suka sace 'yan mata, ta gane wasu daga cikin 'yan makarantar su a hoton video da kungiyar ta fitar.

Bayanan hoto,

'Yan Boko Haram sun afkawa makarantar ta Chibok da ke arewa maso gabashin Nigeria kwanaki 90 da suka wuce, suka sace 'yan mata 276 wadanda ke rubuta jarrabawa.

Bayanan hoto,

Iyayen 'yan mata 'yan makarantar da aka sace har yanzu suna cikin bakin ciki suna kuka manyan kasashen duniya su taimaka wajen ceto 'ya'yansu.

Bayanan hoto,

Mai fafutukar kare ci gaban Ilmin 'ya'ya mata Malala Yousafzai 'yar Pakistan wadda ta tsira daga harbin 'yan Taliban saboda ta na da'awar a baiwa 'ya'ya mata ta na rike da hoton Sarah Samuel wadda yan Boko Haram suka sace.

Bayanan hoto,

Shugaban Boko Haram Abubakar Shekau ya fada a wani sabon video cewa a shirye yake ya tatattauna musayar 'yan matan da fursunoni 'yan uwansu da ake tsare da su.