Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Shari'ar Karim Wade a Senegal

Za a fara shari'a game da wata kara da aka kai Karim Wade, dan tsohon shugaban kasar Senegal, Abdoulaye Wade.

Ana dai zargin dan tsohon shugaban kasar ne da laifin azurta kansa da dukiya ta miliyoyin dalar Amurka ta haramtacciyar hanya.

Sai dai kungiyoyin kare hakkin bil'adama sun bayyana damuwa game da wannan shari'a da za a fara.