Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Labaran duniya na Talbijin

Sashen Hausa na BBC na shirin fara gabatar da shirye shirye ta gidan talbijin, inda a kowace rana daga Litinin zuwa Juma'a zamu dunga kawo muku labarai na yadda duniya ke ciki.

Zaku iya kallon wadannan labarai ta hanyar abokan kawancenmu kamar gidan talbijin na Adom da ke Ghana, ko gidan talbijin na Abubakar Rimi da ke Kano, ko Capital TV a Kaduna, ko kuma Saraounia TV a Jamhuriyar Niger. Haka nan kuma muna fatan kawo muku ta gidan talbijin na AIT.