Taron shugabannin Afrika da Amurka

Taron shugabannin Afrika da Amurka

Shugaban DRC Joseph Kabila
Bayanan hoto,

Tawagogi sun hallara a birnin Washington DC domin halartar taro mafi girma da aka taba yi tsakanin shugabannin Afrika da kuma Amurka. Daga cikin tarukan farko da aka yi sun hada da taro tsakanin shugaba Joseph Kabila na Congo da Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry.

Bayanan hoto,

Taron Kolin dai ya duba yadda za a yaukaka dangantaka tsakanin nahiyar Afrika da kuma Amurka, a yayin da China ke kara zuba jari a nahiyar.

Bayanan hoto,

Kamfanonin Amurka sun yi alkawarin sanya jarin dala biliyan 14 a Afrika, a bangarorin da suka hada da makamashi da samar da ababen more rayuwa, a cewar Shugaban Amurka Barack Obama.

Bayanan hoto,

Shugaba Obama ya kuma dauki nauyin wata liyafar cin abincin dare tare da shugabannin Afrika a fadar White House.

Bayanan hoto,

Shugaban kasar Kamaru Paul Biya da matarsa Chantal na cikin bakin shugaba Obama.

Bayanan hoto,

Shugaban kasar Sudan ta Kudu Salva Kiir na daga wa jama'a hannu a lokacin da ya isa fadar White House.

Bayanan hoto,

Shugaban kasar Gambia Yahya Jammeh ya daga wa masu daukar hoto hannu a lokacin da ya isa fadar tare da matarsa Zineb Jammeh.

Bayanan hoto,

Shugaban Ghana John Mahama shi ma ya halarci liyafar cin abincin da matarsa Lordina Mahama.

Bayanan hoto,

Baki sun cika wani wuri na musamman da aka yi a South Lawn na fadar ta White House, bayan shafe yini guda suna taron cinikayya da ma'aikatar cinikayya ta Amurka.

Bayanan hoto,

Matar shugaban Amurka, Michelle Obama wadda ke daukar nauyin taron tare da mijinta, ta kara kofi da shugabar hukumar tarayyar Afrika Nkosazana Dlamini Zuma.

Bayanan hoto,

Mawaki Lionel Richie ne ya nishadantar da taron jami'an diplomasiyya da sauran manyan baki.