Kwayar cutar Ebola
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Shiri na daya kan Ebola

Hakkin mallakar hoto science photo library
Image caption Kwayar cutar Ebola

Cutar Ebola, cuta ce da a cikin 'yan watannin baya ta barke a Guinea sannan ta bazu zuwa kasashen Liberia da Sierra Leone har ma da Nigeria. Tun lokacin da cutar Ebola ta bayyana, ta hallaka mutane sama da 1,000 a wadannan kasashe.

Kawo yanzu babu wani magani takamaimai na wannan cuta ta Ebola. Wannan na daya daga cikin shiri na musamman da BBC ta shirya akan cutar ta Ebola, da nufin rage hadarin kamuwa da ita, da yadda mutum zai yi idan shi ko wani da ya sani ba shi da lafiya.

A shirinmu na yau, za mu dauko bayani dalla dalla, inda za mu fara da yadda annobar ta fara, da bayani akan ita kanta cutar ta Ebola, da kuma alamun da mutum zai duba idan yana fargabar kamuwa da cutar.