'Yan gudun hijirar Darfur a da da yanzu

Hotunan sansanonin 'yan gudun hijirar yankin Darfur na Sudan da aka dauka a shekarar 2007 sun nuna yadda rayuwa ta canza bayan shekaru bakwai.

Hamisa a sansanin Hassa Hissa na Darfur, Sudan - 2007
Bayanan hoto,

Fiye da shekaru 10 da suka wuce rikici ya barke a Darfur da ke yammacin Sudan, inda mutane fiye da miliyan biyu suka kauracewa gidajensu, kuma babu alamun za su koma gida.

Bayanan hoto,

Hamisa na tuna lokacin da ta tsere daga kauyensu a shekarar 2003 "goye da daya daga cikin jikokinta a baya". Tace "ba ta taba tunanin za ta shafe shekaru 11 a wannan sansanin".

Bayanan hoto,

Mazauna karkara a Sudan galibi manoma ne, amma tashin hankali ya raba su da muhallansu da kuma dabbobinsu.

Bayanan hoto,

An kafa sansanoni fiye da 27 a Darfur inda mutane fiye da 70,000 ke zaune a cikinsu.

Bayanan hoto,

Wasu mutane sun ga wurin zama a sansanonin, inda har an soma siye da sayarwa na abubuwan yau da kullum.

Bayanan hoto,

Amina sanye da koriyar riga a cikin wannan hoton, ta tuna lokacin da suka leka wannan rijiyar shekaru bakwai da suka wuce.

Bayanan hoto,

"Har yanzu muna fuskantar kalubale bayan shafe shekaru 10 a nan, amma dai bamu da matsalar samun ruwan sha," in ji Amina.

Bayanan hoto,

Ana fuskantar matsaloli wajen samun aikin yi a sansanonin, ba kamar lokacin da Yousif ya zo a shekara ta 2007 inda ya koyi yadda ake yin burodi.

Bayanan hoto,

Haja a wannan hoton da aka dauka a shekara ta 2007, ita ce karama daga cikin jikoki bakwai na Horan a sansanin Hassa Hissa.

Bayanan hoto,

Bayan shekaru bakwai, Horan a yanzu ya soma karantun Kur'ani kuma akwai sauran yara a sansanin da ke zuwa makarantar Islamiyya.

Bayanan hoto,

Rawia ta tsere daga kauyensu tare da mijinta da 'ya'yansu amma da 'yar karamar jarka ta tsira, kamar sauran matan kauyensu.

Bayanan hoto,

Rikicin a Darfur ya dauki salo daban daban, inda mayakan sa-kai da 'yan tawaye ke fafatawa da dakarun gwamnati.

Bayanan hoto,

An yi kokarin tabbatar da zaman lafiya a 2011, amma aka gamu da cikas sakamakon dadadden zaman doya da manja tsakanin makiyaya Larabawa da kuma manoman bakar fata.