Shingen bincike na sojoji a Ukraine

Shingen binciken sojoji a kusa da wani gari wanda dakarun gwamnati suka sake kamawa a gabashin Ukraine.

A karamin garin Debalcevo da ke karkashin ikon gwamnatin Ukraine, ana iya jin harbe-harbe da amon bindigogi a ko'ina. A wani yanki mai nisan kilomitoci kalilan daga gabas, nan ne Jamhuriyar al'umma ta abun da ake kira da Lugansk din 'yan-a-ware ta fara, kuma a kudu da yamma da kan iyakar garin, wani yankin 'yan-a-ware ne na DNR.
Bayanan hoto,

A karamin garin Debalcevo da ke karkashin ikon gwamnatin Ukraine, ana iya jin harbe-harbe da amon bindigogi a ko'ina. A wani yanki mai nisan kilomitoci kalilan daga gabas, nan ne Jamhuriyar al'umma ta abun da ake kira da Lugansk din 'yan-a-ware ta fara, kuma a kudu da yamma da kan iyakar garin, wani yankin 'yan-a-ware ne na DNR.

Bayanan hoto,

Akasarin ana fafata fada ne da dare, da rana kuma ana iya ganin fararen hula a kan wannan babban titi da ya nufi Rostov. Fararen hular na da al'adar yi wa motoci ratsin farin fenti. Wasu suna tsere wa fada ne, amma wasu suna kai 'ya'yansu zuwa wani wuri ne a bangarorin biyu a cewar sojoji

Bayanan hoto,

Ana iya hango hanyar motar da ke tsakiyar sararin ciyayi daga ko'ina daga nesa. Galibin motocin a guje suke tafiya don gudun kada a hare su.

Bayanan hoto,

A daren ranar lahadi wannan mota wadda 'yan-a-ware ke ciki bisa kuskure ta tsinci kanta a kusa da shingen binciken Ukraine. 'Yan-a-ware biyu sun tsere lokacin da suka ji harbin gargadi, amma ban da direban wanda ya so koma wa da baya. Sojojin Ukraine sun bude wa motar wuta, nan kuma gobara ta kama. An kama direban bayan an yi masa magani saboda raunukan da ya ji.

Bayanan hoto,

Da rana, gari yakan nutsa, sojoji suna iya sararawa duk da amon fashewar rokoki da ake ji nan da can. Wani bakon abu kuma shi ne yadda dakarun tsaron kasa ke cikin tsimi, inda za ka ji suna raha a kan harbin rokar daren jiya na bindigar GRAD ta Rasha mai zafin harbi

Bayanan hoto,

Da kwallewar ranar bazara za ka ga sojojin Ukraine cikin farin ciki sun je sayen askirin a wani kanti da ke gefen hanya

Bayanan hoto,

Wani yaro kenan a kan keke da ya ce ba ya jin wani tsoro, inda yake zuwa neman kwanson harsasai yana ciccire su

Bayanan hoto,

Komai a nan-kama daga manyan motocin sulke zuwa hulanan kwano da rigunan sulke ana musu ado da shagube ga Putin na wata waka da ta yi kaurin suna ko taken kishin kasa na "Ukraine ce gaba da komai". Sojoji da dama sun mayar da yin tambari da alamar kishin Ukraine a jikinsu wata sara.

Bayanan hoto,

Sojoji suna gwada sabbin kayayyakin da 'yan sa-kai suka saya musu- kayan soji masu hatsa-hatsa da kayan aiki na musammam, gilasan hular kwano. Sojojin sukan ce a isar da godiyarsu ga 'yan sa-kan. Duk abun da muke da shi za mu sadaukar ga rayuwar jama'a.

Bayanan hoto,

Wani dakaren tsaron kasa a kusa da Kiev, da ba ya shayin a dauke shi a hoto. Galibin mutane ba sa son tsayawa a gaban kyamara. Hakan ka iya zama abu mai hatsari ga jami'an leken sirri. Wasu kuma ba sa so don kada matansu su san inda suke. Akasari suna yi wa danginsu karyar cewa suna wani wuri cikin aminci nesa da inda ake yaki.

Bayanan hoto,

Yawan ababen hawan da za a gani a kan titi ya dogaro ne kan harkokin da ke gudana a yankin. Ana barin motocin fararen hula su ci gaba da zirga-zirga har zuwa ko dai karfe 6 na yamma ko 11 na dare agogon yankin.

Bayanan hoto,

Duk da luguden rokoki da harbe-harben bindiga a titunan yankin, motocin safa sun ci gaba da sufuri tsakanin birane.