Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Gane Mani Hanya 30/08/14

Hukumar kwallon kafa ta Nigeria NFF na fama da rikice-rikice wanda hakan ke haifar da matsaloli wajen gudanar da harkokin kwallon kafa a kasar.

Ko a ciki wannan shekarar sau biyu hukumar kwallon kafa ta Duniya FIFA na dakatar da Nigeria daga shiga harkar wasan kwallon kafa, saboda dakatar da Shugabanta da mambobin hukumar suka yi daga kan aikinsa da kuma sauke shi daga mukaminsa da wata kotu a Jos, babban birnin jihar Filato tayi.

Ranar talatar da ta gabata ne hukumar ta shirya babban taronta na kasa a Abuja, wanda shi ma ya bar baya da kura.

A cikin shirinmu na Gane mini hanya na wannan makon, Mohammed Abdu ya yi mana nazari kan rikita-rikitar da hukumar kwallon kafa ta Nigeriar ta tsinci kanta a ciki, ga kuma rahoto na musamman da ya hada mana: