Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Shiri na bakwai kan Ebola

A yanzu dai matsalar cutar Ebola ta bulla kasashe akalla biyar a yankin Afirka ta yamma, wadanda suka hada da Gini da Saliyo da Liberiya da Najeriya, a yanzu kuma kari da kasar Senegal.

Adadin mutanen da suka mutu a sanadiyyar wannan cuta kuma ya haura dubu daya da dari biyar.

Sai dai wata babbar tambaya da kasashen da abin ya shafa suke kokowa da ita a yanzu, ita ce shin ta ya za' a dakatar da yaduwar cutar?

Bakin hukumar lafiya ta majalisar dinkin duniya (WHO) dana kwararru a fannin kiwon lafiya yazo daya, cewa amsa mafi tasiri game da hakan, ita ce a ware wadanda ake jin sun kamu da cutar, har sai hukumomin kiwon lafiya sun kai dauki gare su.