Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Gane Mani Hanya 06/09/14

A yayinda kungiyar Boko Haram ke kara karbe iko da garuruwa a jihar Borno a Najeriya, tsohon Gwamnan Jihar, Sanata Ali Modu Shariff ya musanta zarge-zargen cewa yana da alaka da kungiyar.

A kwanakin bayane wani dan kasar Australia da ya ce ya taba yunkurin shiga tsakani da kungiyar a madadin gwamnatin Najeriya.

Ya kuma yi zargin cewa kokarin sasantar, wasu kwamandojin Boko Haram sun shaida masa cewa tsohon gwamnan na daga cikin masu taimaka masu.

To Sanata Ali Modu Shariff din ya ziyar ci ofishinmu na Abuja a kwamankin baya, inda ya bukaci a bashi daman yin raddi, ga dan Australian, dama wasu dake dangan tashi da kungiyar Boko Haram.

An hada shi ta layi da Jimeh Saleh a London, wanda ya fara da tambayar sa irin martanin da zai mayar akan zargin.

Ga kuma karashen hirar a filin Gane Mani Hanya na wannan makon