Kaddamar da shirin talabijin na BBC Hausa

Sashen Hausa na BBC ya fara gabatar da labaransa ta kafar talabijin, a wani abu da shi ne irinsa na farko ga tashoshin watsa labarai na duniya.

Karfe tara na dare a ranar Litinin, 8 ga Satumbar, 2014 a dakin watsa shirye-shiryen talabijin na BBC da ke London, ranar da aka kadammar da shirin talabijin na BBC Hausa.
Bayanan hoto,

Karfe tara na dare a ranar Litinin, 8 ga Satumbar, 2014 a dakin watsa shirye-shiryen talabijin na BBC da ke London, ranar da aka kadammar da shirin talabijin na BBC Hausa.

Bayanan hoto,

Babban mai tsara shiri, Elhadji Diori Coulibaly da Jimeh Saleh da kuma Nick Barkley a lokacin da ake gabatar da shirin talabijin.

Bayanan hoto,

Editan talabijin na sashin harsuna a BBC, Ian Haddow da Shugabar kulla da ayyukan jarida na BBC, Nikki Clarke da Editan Afrika, Solomon Mugera a lokacin kaddamar da shirin talabijin na BBC Hausa

Bayanan hoto,

Wasu daga cikin masu lura da shirye-shiryen talabijin na BBC, Kevin Oliver a hagu da kuma Tony Cook.

Bayanan hoto,

Ma'aikatan BBC da dama sun kalli shirin lokacin da aka kaddamar a talabijin. Iliya Djadi da Ahmed Abba Abdullahi da Issa Didier Kouame da kuma Ibrahim Isa.

Bayanan hoto,

Mai bada umurni na shirin talabijin, Nick Barkley tare da mai gabatar da shirin talabijin na BBC Hausa, Aichatou Moussa.

Bayanan hoto,

Mai gabatar da shirin talabijin na BBC Hausa, Aichatou Moussa tare da maigidanta da 'ya'yanta a cikin dakin watsa shirye-shirye.

Bayanan hoto,

Ma'aikatan sashin Hausa na BBC, Aliyu Abdullahi Tanko tare da Aichatou Moussa lokacin da ake kamalla gabatar da shirin talabijin.

Bayanan hoto,

Suwaiba Ahmed na daga cikin wadanda suka kalli yadda aka gabatar da shirin BBC Hausa na farko a talabijin.

Bayanan hoto,

Wasu daga masu lura da shirye-shiryen talabijin na BBC, Mehvish Hussain da kuma Jeane McCallum.

Bayanan hoto,

Ma'aikatan da dama sun yi murna bayan samun nasarar kaddamar da shirin talabijin na BBC Hausa.

Bayanan hoto,

Daga ranar Litinin zuwa Juma'a za a dunga gabatar da shirin talabijin na BBC Hausa. Za ku iya kallon shirin a shafinmu na bbchausa.com da kuma wasu tashoshin talabijin a wasu kasashen Afrika.