Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

'Rayuwa a matsayin Sarkin Kano'

A cikin watan Yuni ne Sarkin Kano Mai Martaba Muhammadu Sanusi na biyu ya hau kan karagar mulkin Kano, bayan rasuwar Sarki Ado Bayero.

Hawan Sarki Muhammad Sanusi na biyu kan karagar mulkin Kano ya janyo kace-nace, kafin daga bisani kura ta lafa, har ya samu shiga fada, mako guda bayan nada shi.

Editan Sashen Hausa na BBC Mansur Liman, ya ziyarci fadar ta Kano, inda ya tattauna da Sarki Muhammadu Sanusi na biyu, domin fara shirin BBC Hausa na Talabijin. Ya fara ne da tambayarsa yadda ya ji bayan nada shi Sarkin Kano;