Dole ne a yi zabe a 2015 - Atiku

A Najeriya, yayin da wasu ke tababa game da yiwuwar gudanar da babban zabe a badi, saboda rikicin Boko Haram, tsohon mataimakin shugaban kasar, Alhaji Atiku Abubakar, wanda ake sa ran a makon gobe zai bayyana takarar shugabancinsa a zaben mai zuwa, ya shaidawa BBC cewa, da ma gwamnatin Najeriyar ba ta son a yi zaben.