An dakatar da Benoit Assou-Ekotto

Benoit Assou-Ekotto
Bayanan hoto,

Benoit Assou-Ekotto

An dakatar da dan kwallon Tottenham, Benoit Assou-Ekotto na wasanni uku saboda aikata ba daidai ba wajen nuna goyon baya ga Nicolas Anelka.

An kuma bukaci Assou-Ekotto mai shekaru 30 ya biya tarar fan dubu 50 saboda kalaman da ya rubuta a shafukan zumunta na zamani.

Tuni aka dakatar da Anelka na tsawon wasanni biyar da kuma tarar fan dubu 80 saboda yin wata alama da hannunsa wanda ake zargin na nuna wariya ce.

A lokacin sai Assou-Ekotto ya yi amfani da Twitter wajen taya Anelka murnar wannan matakin.