Ra'ayi Riga: Cece-kuce kan zaben 2015

A Nijeriya wani batu da ya taso, bayan komawar zaman majalisar dattawa shi ne furucin da shugaban majalisar yayi cewa kasar na cikin yanayi na yaki.

Sakamakon artabun da ake yi da 'Yan boko Haram a arewa maso gabashin kasar.

An ambaci mataimakin shugaban majalisar yana cewa, sashe na dari da talatin da biyar na kundin tsarin mulkin Najeriya ya bayar da damar a dage lokacin gudanar da zabe matukar wani yanki na Nigeria na fama da yaki, kuma shugaban kasa ya yanke shawarar cewa ba za a iya gudanar da zaben ba.

Ya kuke ganin wannan dambarwa, ko yanayin da ake ciki ya sa kun fara shaku game da yuwuwar zabe a wadannan yankuna? wasu kenan daga cikin batutuwan da muke fatan tattaunawa a filinmu na Ra'ayi Riga.