Hotunan Masallatai da coci-coci na tarihi

Tsare-tsaren gine-gine na addini su ne suka fi nuna tarihin turawan mulkin mallaka da kuma yadda suka yada al'adunsu, sannan su ma suka koyi al'adun mutanen da suka mulka fiye da irin gine-ginen da suka yi amfani da su wajen gudanar da mulki.

Masallacin Hoja Imam da ke Samarqand
Bayanan hoto,

Kamar sauran masallatai irin na karkara, shi ma masallacin Hoja Imom an yi amfani da shi a matsayin wajen tattauna wa na mutanen karkara a lokacin tsohuwar Tarayyar Soviet. Yanzu kuma ana yin sallah a cikinsa, da taro da shan shayi, lamarin da ke nuna yadda tsarin musulinci ya sauya a nahiyar Asia. An gyara masallacin a shekarar 2010, kuma an mayar da tsofaffin katakwayensa domin mutane su ga irin yadda zamani ya yi tasiri a kansa. Ana samun irin wannan ado da ake yi da irin wannan katako da ake kira vassa a gidajen Turawan mulkin mallaka, musamman 'yan kasuwar kasar Rasha da ke Tashkent da Samarkand.

Bayanan hoto,

A cewar wata taswirar da ke yi wa matafiya bayani mai suna Lonely Planet Travel Guide, masallacin Hazret-Hyzr shi ne masallaci ' mafi kyawu a Samarkand', wanda aka gina a shekarar 1854. An gina shi a wurin da Genghis-Khan ya taba gina wani masallaci a karni na takwas kodayake an rusa shi daga baya. An yi ta sake gina masallacin a lokuta daban-daban, musamman a tsakanin shekarun 1990. Daga masallacin ana iya hango yadda tsohon garin ke da kyawu.

Bayanan hoto,

Masallacin Hoja Imom da ke Samarkand yana daya daga cikin masallatai da aka gina a sassa daban-daban na tsofaffin garuruwan tsakiyar nahiyar Asia a karni na goma sha tara. An gina shi ne da tsofaffin katakwaye, kana aka yi wa rufinsa ado, sannan aka tare shi da ginshikai masu kwari.

Bayanan hoto,

Wannan kawataccen masallacin da ke yankin Urgut mai cike da tsaunuka, kilomita 40 a kudancin Samarkand, ya yi kama da ginin Timurid da ke da matukar girma, sai dai wannan an gina shi ne a karshen karni na goma sha tara da bululluka irin na kasar Rasha. An gina masallacin ne a wani tsohon wajen tarihi na Chor Chinor, inda tsofaffin bishiyoyi da kaburburan sufaye suke.

Bayanan hoto,

An gina majami'ar St Alexiy ne a shekarar 1912 domin sojin Rasha wadanda suka yi sansani a barikin Cossack da ke Samarqand. Wannan babbar majami'a ita ce majami'ar Orthodox ta St. Alexis mafi girma a Samarkand, kuma wata manuniya ce tsakanin yadda ake sson yin gini irin na Rasha a farkon karni na 20 da kuma yadda ake son yin gine-gine da bulo da gorar-ruwa. Mai zane-zane F. Smirnov ne ya gina majami'ar , kuma an kwashe shekaru da dama ana yin amfani da shi a matsayin wajen yin taron wata babbar bataliyar soji da ke tsakiyar birnin. An mayar da ita coci ne a shekarar 1996 sai dai 'yan kasar Rasha kalilan ne ke zuwa cikinta domin yin bauta.

Bayanan hoto,

Har yanzu 'yan Armenia masu dimbin yawa na zaune a Samarkand, kuma sun gina cocin Gregori ta 'yan Armenia ta farko a birnin ne a shekarar 1903. An sanya wa cocin sunan St. Astvatsatsin (Mutuniyarmu). Bayan da aka samu 'yanci ne aka sake mayar da ita coci, kana aka inganta gininta. A cocin ake koyawa 'yan Armenia darussa sannan ake gudanar da shafin intanet dinsu. Har yanzu 'yan Armenia masu dimbin yawa na zaune a Samarkand, kuma sun gina cocin Gregori ta 'yan Armenia ta farko a birnin ne a shekarar 1903. An sanya wa cocin sunan St. Astvatsatsin (Mutuniyarmu). Bayan da aka samu 'yanci ne aka sake mayar da ita coci, kana aka inganta gininta. A cocin ake koyawa 'yan Armenia darussa sannan ake gudanar da shafin intanet dinsu. Har yanzu 'yan Armenia masu dimbin yawa na zaune a Samarkand, kuma sun gina cocin Gregori ta 'yan Armenia ta farko a birnin ne a shekarar 1903. An sanya wa cocin sunan St. Astvatsatsin (Mutuniyarmu). Bayan da aka samu 'yanci ne aka sake mayar da ita coci, kana aka inganta gininta. A cocin ake koyawa 'yan Armenia darussa sannan ake gudanar da shafin intanet dinsu.

Bayanan hoto,

Ginin jan bulo da aka yi wa majami'ar St. Alexis ya sa ta zama mai kyawu sosai. Hakan ya sa ta hada salon ginin Rasha da ake yi da bulo zalla, watau irin ginin da ake kira na Trukestan. A wasu lokacin 'yan kasar ba sa iya bambanta majami'ar St. Alexis Cathedral da majami'ar Katolika ta St. John, wacce ke kusa da ita.

Bayanan hoto,

A lokacin mulkin shugaban tsohuwar Tarayyar Soviet Nikita Khrushchev ne ya rufe Cocin St George Church, wacce dan Rasha, Tzar, ya gina a shekarar 1882. Ya rufe ta ne domin yin adawa da harkokin addini.