Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Makarantar koyon kwallon kafa

A kan titunan biranen Afirka, yara masu fatan shahara a kwallon kafa na baje kolin basirarsu ta hanyar kwaikwayon gwanayensu irin su Didier Drogba, ko Samuel Eto'o, ko Michael Essien. Wadanda suka yi sa'a a cikinsu kan samu shiga cibiyoyin horar da kwallon kafa, wadanda ba kawai kwallon suke koyarwa ba, su kan kuma bude kofofin wasu harkokin rayuwa ga yaran idan burinsu na zama 'yan kwallo bai cika ba. Daya daga cikin wadannan cibiyoyi da suka fi dadewa a Afirka ita ce Cibiyar Koyar da Kwallon Kafa ta Afirka ta Yamma, wacce zuwa farkon bana aka fi sani da Feyenoord, a Ghana. BBC ta samu ganawa da wasu daga cikin gwanayen kwallo na gobe.