Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ra'ayi Riga: Yaki da jahilci a Nigeria

Masu iya magana na cewa ilmi gishirin zamani.

Mai yiwuwa wannan dalili ne ya sa hukumomi a ko'ina cikin duniya ke tashi haikan wajen ganin sun ilmantar da wadanda ba su samu cin gajiyar ilmin yayinda suke da kuruciya ba.

Kwanakin baya ne a lokacin bikin ranar yaki da jahilci ta duniya, aka ambaci wata jami'ar gwamnati a Nijeriya tana cewa bincike ya nuna akwai magidanta kimanin miliyan 64 da ba su iya karatu da rubutu ba a kasar.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da hukumomi ke cewa suna son ganin kowa ya samu ilmin daga nan zuwa badi.

Shin ya wannan lamari na yaki da jahilci yake a yankunanku, kuma wadanne matsaloli ake fuskanta, kana kuma wadanne matakai suka kamata a dauka na inganta karatun manyan? Wasu kenan daga cikin batutuwan da zamu tattauna a kan su a filin namu na Ra'ayi Riga.