Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Gane Mani Hanya 01/11/14

A wannan satin muka kawo maku hirarrakin da muka yi da wasu 'yan matan Chibok uku, wadanda su ka kubuta daga hannun 'yan Boko Haram.

Fiye da watanni shidda kenan da 'yan Boko Haram din su ka je makarantar 'yan matan a Chibok, kuma su ka yi awon gaba da dukansu.

Har yanzu akwai fiye da dari biyu da ke hannun 'yan Boko Haram din.

To Aichatou Moussa ta yi hira da daya daga cikin iyayen yaran, wanda ba za mu bayyana sunansa ba saboda dalilan tsaro. Ya fara ne da gaya mata yadda ya sami labarin cewa an sace 'yan matan, ciki har da diyarsa: