Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ra'ayi Riga:Baki biyu kan sulhu da Boko Haram

A kwanakin baya ne wata kafa ta gwamnatin Najeriya ta ce an cimma yarjejeniyar tsagaita wuta da 'yan kungiyar Boko Haram, har ma akwai yiwuwar sako 'yanmatan Chibok cikin mako guda.

Sai dai kuma bayan da jagoran Boko Haram, Abubakar Shekau, ya fitar da bidiyonsa na baya-bayan nan yana musanta ikirarin gwamnatin Najeriyar, sai ga wani bangaren gwamnatin kuma yana cewa da ma ba a fahimce su ba ne, ba su ce sun cim ma yarjejeniyar tsagaita wutar ba, lamarin da ya sa mutane da dama zargin gwamnatin da yawan yin amai ta lashe.