Nasarori a yaki da cutar Polio

Cibiyar yaki da cututuka ta Amirka ta yi amunnar an cimma wani mahimmin mataki wajen neman kawar da cutar shan inna ko polio.

Kwararru a cibiyar na jin cewa, an kawar da nau'i na biyu daga cikin nau'o'i uku na polion, sakamakon rigakafin gama-gari.

Suka ce fiye da shekaru biyu kenan da ba a ga nau'in ba. Ga rahoton Elhadji Diori Coulibaly