Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Mayakan Al-Shabaab sun hallaka 'yan Kenya

Wasu mayakan al Shabaab sun tsallaka cikin Kenya inda suka hallaka mutane talatin da shidda da ke aikin fasa dutse a kusa da garin Mandera na Arewacin kasar. A wannan yanki ne dai aka kashe wasu mutanen ashirin da takwas, kasa da makonni biyu da suka wuce. Shugaba Kenyatta, ya kori ministan cikin Gida, kuma Sufeto Janar na 'yan sanda ya yi murabis. Ga rahoton Isa Sanusi.