Shekara daya da mutuwar Nelson Mandela

'Yan Afrika ta Kudu na bukukuwan cika shekara daya cif-cif da mutuwar tsohon shugaban kasar, Nelson Mandela. Shi ne ya taimaka wajen mayar da kasar bisa turbar Demokradiyya daga mulkin wariyar launin fata. Ana bukukuwan ne a sassa daban-daban na kasar, ciki har da garinsa na haifuwa, Qunu dake lardin Gabashin Cape. Ga dai rahoton Isa Sanusi.