Yanayin da ake ciki a garin Mubi na Adamawa

A ranar 29 ga watan Okotoba ne 'yan kungiyar Boko Haram sun kame garin Mubi na jihar Adamawa, har ma sun kafa tutarsu daga bisani suka kafa dokar hana fita ko shiga garin.

A ranar 29 ga watan Okotoba ne 'yan kungiyar Boko Haram sun kame garin Mubi na jihar Adamawa, har ma sun kafa tutarsu daga bisani suka kafa dokar hana fita ko shiga garin.
Bayanan hoto,

A ranar 29 ga watan Okotoba ne 'yan kungiyar Boko Haram sun kame garin Mubi na jihar Adamawa, har ma sun kafa tutarsu daga bisani suka kafa dokar hana fita ko shiga garin.

Bayanan hoto,

A tsakiyar watan Nuwamba ne gwamnatin jihar Adamawa ta sanarda kwace garin Mubi daga hannun Boko Haram, tare da gudunmuwar sojoji da mafarauta da 'yan civilian JTF.

Bayanan hoto,

Duk da cewa sojojin Nigeria sun kwato garin Mubi, amma har yanzu saboda tsoro da yanayi na rashin tabbas mutane sun ki so koma gidajensu.

Bayanan hoto,

Wasu jama'a sun koma garin Mubi, har an soma cin kasuwa, sai dai dubban mutane sun riga sun koma wasu garuruwa kuma sun su koma gidajensu.

Bayanan hoto,

Sarkin Mubi, Alhaji Abubakar Isa Ahmadu ya fice zuwa birnin Yola lokacin da 'yan Boko Haram suka kwace garin, amma a yanzu jami'an tsaro sun kwato garin.

Bayanan hoto,

Kungiyar Boko Haram ta sauya sunan garin Mubi zuwa "madinatul Islam". Mazauna garin sun ce 'yan kungiyar suna amfani da dokokin addinin musulunci.