Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Malala ta samu kyautar Nobel

Malala Yousafzai - yarinyar nan 'yar Pakistan da 'yan Taliban suka harba - ta zama mutum mafi kankantar shekaru da ya taba samun kyautar Nobel ta zaman lafiya. Tun tana da shekara sha daya take fafutukar ganin mata sun sami ilimi a Pakistan. Malalar ta sami kyautar ce tare da Kailash Satyarthi, mai kare hakkin kananan yara a India. Ga rahoton Isa Sanusi: