Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Zabiya na fuskantar barazana a Tanzania

An kaddamar da wani babban kamfen a Tanzania, a karkashin jagorancin shugaban kasar, don neman kudaden da zasu taimaka wajen kare zabiya, wadanda ake ba mafaka a tsibirin Ukerewe. A 'yan shekarun nan yawan zabiyar da ake kashewa a kasar ya karu. Masu kisan suna yin tsafi ne da sassan jikinsu, da zummar yin arziki. Ga Elhadji Diori Coulibaly da karin bayyani.