Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ana ci gaba da zaman makoki a Pakistan

An kwashe yinin yau ana zaman makoki da addu'o'i a Pakistan, da kuma jana'izar mutanen da aka yiwa kisan kare dangi a wata makaranta, a birnin Peshawar. Akalla yara dari da talatin da biyu, da kuma manya guda tara ne 'yan Taliban suka hallaka a harin. Praminista Nawaz Sharif yayi alkawarin kawar da ta'addanci daga Pakistan din. Ga rahoton Isa Sanusi: