Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Mayakan IS sun kama matukun jirgin yakin Jordan

Mayakan kungiyar IS, sun kama wani matukun jirgin yakin Jordan, bayan jirginsa ya yi hadari a cikin Syria. IS din ta ce ta harbo jirgin ne da wani makami mai linzami. Idan hakan ta tabbata, wannan zai kasance karon farko da kungiyar ta IS ta kabo wani jirgin kawancen da Amurka ke jagoranta. Jordan dai ta ce lamarin ba zai sa ta fice daga kawancen ba. Ga dai rahoton Ibrahim Isa