Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

AirAsia: An tsamo gawawwaki 40 a tekun Java

Yanzu dai kusan gawaki arba'in ne aka tsamo daga tekun Java, bayan hadarin jirgin saman nan na Air Asia a makon jiya.

Sai dai har yanzu ana cigaba da neman nau'rorin nadar bayanan jirgin, wadanda za su iya taimakawa wajen sanin musabbabin hadarin.

Dukan fasinjoji 162 da ma'aikatan jirgin sun hallaka a hadarin. Ga rahoton Isa Sanusi: