Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Hari a mujallar Charlie Hebdo a Faransa

'Yan sanda a Faransa sun ce 'yan bindiga sun hallaka mutane akalla goma sha biyu a ofishin wata mujallar barkwanci mai suna Charlie Hebdo.

An kuma bayyana cewa wasu mutane biyar sun samu munanan raunuka a harin.

Lamarin ya faru ne da safiyar ranar Laraba inda 'yan bindigar da fuskokinsu a rufe suka kutsa cikin ginin sannan suka yi harbi kusan sau hamsin kafin su gudu a cikin mota.

(DAGA INSTAGRAM AKA SAMU BIDIYON)