Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

'Yan Boko Haram sun yi barna a Baga

A Najeriya shugaban karamar hukumar Kukawa a Jihar Borno, Alhaji Musa Alhaji Bukar Kukawa ya ce 'yan Boko Haram sun sake kai wani harin a garin Baga. Ya ce yawan mutanen da aka kashe a harin farko da kungiyar ta kai a kan garin a ranar Asabar zai kai dubu biyu.To Mohammed Kabir Mohammed a Abuja, ya tuntubi Saneta Maina Ma'aji Lawal, dan majalisar Dattawa mai wakiltar arewacin Borno, don jin karin bayani: